Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar


A yau Lahadi, 1 ga watan Maris ne al’ummar Musulmi suka yi sallar idi a Jamhuriyar Nijar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a kasar, lamarin da ya kawo karshen azumin Ramadana a kasar, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Al’ummar kasar daga bangarori daban-daban sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal a daren ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu, inda majalisar koli ta musulunci da gwamnatin kasar suka tabbatar da hakan bayan gudanar da cikakken bincike.

Ba a yi sallah ba a kasashe da dama ciki harda Saudiyya da Najeriya sakamakon rashin ganin wata. Hakan na nufin sai gobe Litinin za a sallaci idi a kasashen.

A hotunan da BBC Hausa ta wallafa, an gano al’ummar musulmi manya da yara a masallacin idi cikin shiga ta alfarma.
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN