Da dumi-dumi: Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a ajiye Azumi


Shararren malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa muddin aka samu mutum fiye da biyar adilai a garuruwa da suke kusa da juna sun ga wata, to za su ajiye azumi. Aminiya ta ruwaito.

Malamin ya bayyana haka ne lokacin da wasu suka tuntube shi a Madina, suna shaida mishi cewa akalla mutum biyar sun ga watan Shawwal (na Karamar Sallah) a ranar Asabar a Abuja, wasu kuma sun gani a Doma cikin Jihar Nassarawa da kuma Kurgwi a Jihar Filato.

Sheikh Dahiru, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Fatawa a Majalisar Koli Kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeria ya ce, “Ba mu da ikon karyata su.

“Wanda ya samu labari zai ajiye azumi, sai dai wanda bai ji ba, amma Sallar Idi, tun da nafila ce a je a yi da sauran jama’a,” a cewarsa.

Malamin ya bayyana cewa, “Adadin shaida mutum hudu ne a Musulunci; in sun kai mutane biyar ko fiye an samu jama’a masu yawa — Za a sha ruwa.

“Wadannan shaidun da aka bayar duka mun yarda da su, domin daga mutanen gari daya sun kai biyar. To wata ya tabbata, balle wuri biyu ko uku.

“Saboda haka ba mu da wata hujjar da za mu karyata su, domin sai ka mayar da mutum fasiki ka karyata shi ganin wata. Wadannan mutane yaya za mu mayar da su fasikai?”

Fatawar malamin na zuwa ne bayan Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya sanar Asabar cewa za a cika azumi 30 saboda ba a ga watan Shawwal ba a ranar.

Bayan masu ikirarin ganin watan a Abuja sun gabatar mishi da sunayen mutum shida da suka ce sun gani da idonsu, Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi karin haske da cewa, “Adadin shaida mutum hudu ne a Musulunci; in sun kai mutane biyar ko fiye an samu jama’a masu yawa ke nan.

“Ba mu da ikon karyata su, sai dai in fasikai ne, kuma ba mu da hujjar da za mu ce su fasikai ne.”

Tun lokacin da aka fara amfani da ba da sanarwar ganin wata ta hanyar kimiyya ake samun sabani tsakanin wadansu malamai da Fadar Sarkin Musulmi.

Ana iya tunawa cewa bara, Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi sallar idi sabanin ranar da Sarkin Musulmi ya sanar.

Malamin ya ce ya yi hakan ne bayan ya samu sanarwar ganin wata kuma ya nemi Sarkin Musulmi a sanar da shi ba a same shi ba.

Sheik Dahiru Bauchi ya ce, “Umarnin da Annabi mai tsira da aminci ya bayar shi ne ‘Ku yi azumi in an ga wata, ku sha ruwa in an ga wata, amma in watan ya buya, ku cika kwana 30’, kuma an samu wadanda suka gani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN