Mun jiyo cewa wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saÉ“a wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr.
Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.
Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi.