Yanzu yanzu: Yan sanda sun jaye kara da suka shigar kan kananan yara a gaban Kotun jihar Kebbi , Alkali ya sallami yaran (Hotuna)Alkalin Kotun Sharia da ke Nassarawa 1 a garin Birnin kebbi ya sallami Yara kanana da yan sanda suka gurfanar a gaban Kotu. Shafin isyaku.com News ya wallafa.

Yayin da aka fara sauraren karar tuhumar da ake yi wa yaran da karfe 2:58 na ranar Litinin 9 ga watan Mayu, kwatsam dan sanda mai gabatar da kara ya gaya wa Kotu cewa bisa umarnin Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi yan sanda sun jaye karar da suke yi wa yaran a gaban Kotu.

Bayan yar muhawwarar da lauyoyi wadanda ake dara da dan sanda mai gabatar da kara kan ayoyin doka da suka dogara wajen neman wajabcin wasu ka'idodin sharia, daga karshe dai Alkali ya amsa bukatar da dan sanda mai gabatar da kara ya yi kuma Alkali ya sallami shari'ar.

Idan baku manta ba, mun kawo maku cewa Yan sanda sun gurfanar da yaran ne ranar 20 ga watan Aprilu a gaban Kotu bisa zargin satar wayar wuta a gidan wani Safeton yan sanda a garin kamba, Wanda yaran sun musanta a wani faifen bidiyo.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN