Buhari ya gargadi Sojoji yayin da ‘Yan Bindiga suka kashe mutane da dama a Zamfara, duba abin da ya ce
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi mahukuntan sojoji da kada su yi kasa a gwiwa wajen yakar ‘yan fashin daji yayin da yake mayar da martani game da kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa dimbin mutanen kauyuka a karshen mako. Daily trust ta ruwaito.

Ya ce kwanakin da ’yan fashin daji ke yin yadda suka ga dama ba za a bar su su dawo ba. 

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar jiya, biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Sabon Garin Damri da Kalahe da ke karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara tsakanin Juma’a zuwa Asabar inda aka kashe mutane 40 zuwa 56. 

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun isa Sabon Garin Damri ne a ranar Juma’a a kan babura da dama, inda suka rika harbin mutane. Sun kuma kai hari a wani asibiti da ke unguwar tare da rusa shi. 

“A Sabon Garin Damri, sun kashe akalla mutane 26. Daga nan ne ‘yan bindigar suka koma kauyen Kalahe suka kashe sama da mutane 10 a can. A tsakanin wadannan al’ummomi biyu, an gano akalla gawarwaki 40,” wani mazaunin garin mai suna Aminu Yusuf, ya shaida wa Aminiya . 

Wakilinmu ya tattaro cewa an yi jana’izar akalla mutane 43 da aka kashe a hare-haren. 

Makwanni biyu da suka gabata, sama da 10 daga cikin ‘yan bindigar ne sojoji suka kashe bayan wani artabu da suka yi. 

Sojojin sun dakile wani hari da aka kai wa al’ummar Bakura inda suka yi nasarar kame wasu garken shanu da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su. 

Babu tabbas ko harin na karshen mako na ramuwar gayya ne na kashe masu aikata laifuka 10.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. 

Har yanzu dai rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar Zamfara ba su fitar da wata sanarwa ga jama’a kan kashe-kashen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. 

Buhari, a cikin sanarwar, ya yaba wa sojojin bisa hare-haren da suke kai wa ba tare da bata lokaci ba, yayin da suke ci gaba da samun sakamako mai kyau a yankin Arewa maso Yamma, musamman jihar Zamfara, wadda ta kasance matattarar miyagun ayyuka. 

Ya ce bisa ga dukkan alamu an samu kwanciyar hankali a jihar, inda al’amura suka koma yadda suke a mafi yawan sassan yankunan karkara kuma a shirye suke su sake gudanar da rayuwarsu kamar yadda aka saba. 

Sai dai shugaban kasar ya ce an samu sabani da dama, musamman ganin harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Damri, Sabongarin Damri da Kalahe da kuma Maradun, inda aka samu asarar rayuka da dama. 

“Bai kamata mu bari a dawo kwanakin da ‘yan fashin suka samu damar yin yadda suka ga dama ba. Dole ne a bar mutanen karkara a Zamfara da sauran wurare su samu zaman lafiya. 

"Saboda haka, dole ne a ci gaba da aikin da aka samu don kawo karshen ayyukan wadannan masu kisan kai," in ji shugaban. 

Buhari wanda ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa da gwamnati da al’ummar jihar, ya ce dole ne a hada kai da gwamnatin tarayya da na jihohi su yi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen munanan kashe-kashe cikin gaggawa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN