Yanzu yanzu: Ƴan ta'addan ƙasar Kamaru sun shigo Najeriya, sun bindige rayuka 20

 


Tsagerun Ambazonia, wata kungiyar 'yan aware ta kudu maso yammacin kasar Kamaru, ta halaka rayuka a kalla 20 a cikin al'ummar karamar hukumar Boki ta jihar Cross River a Najeriya. Legit ta ruwaito.

Chief Cletus Obun, tsohon dan majalisar jihar Cross River kuma dan takarar kujerar majalisar wakilai ta Boki da Ikom ne ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ranar Lahadi.

"Zan iya tabbatar mu ku da cewa sojojin Ambazonia sun tsallako iyakar Najeriya a safiyar Lahadi inda suka kai farmaki ga wasu 'yan kasar su da suka ki shiga tsarin su."

"Sun halaka kusan mutum 20, har yanzu babu wanda ya tabbatar da cewa ko akwai 'yan Najeriya cikin wadanda suka halaka," ya ce.

Ya ce ragowar 'yan kasar Kamarun wadanda su ke yin yaren Bokye na jama'ar Boki sun cika yankin Bashu, wani gari da ba shi da nisa da Danare, inda dakarun sojin Najeriya ke da karamin sansani, Daily Trust ta ruwaito.

Tsagerun Ambazonia su kan shiga Boki, inda akwai 'yan kasar Kamaru da yawa kuma su tada tarzoma.

A yayin da aka tuntubi jami'in yada labarai na birged ta 13 na sojin Najeriya da ke Kalaba, Kyaftin Tope Aluko, ya ce har yanzu ba su tabbatar da farmakin ba, wanda ya auku watanni shida bayan makamancinsa a jihar Taraba.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Emmanuel Bwacha, ya koka kan yadda wasu da ake zargin tsagerun kasar Kamaru ne suka halaka dagacin kauye da wasu mazauna yankin Manga da ke Taraba.

Dan majalisar ya ce 'yan awaren kasar Kamaru sun kone kauyen baki daya.

Bwacha, wanda ke wakiltar Taraba ta kudu a majalisar dattawa, ya ce kutsen 'yan awaren barazana ce ga karfin ikon Najeriya na kasantuwar ta kasa tunda har yanzu ba a san dalilansu na yin hakan ba.

Ya ce, "Na tashi a safiyar yau domin in janyo hankulan 'yan kasar mu ballantana cibiyoyin tsaronmu kan mummunan lamarin da ke zagin kasa ga zaman mu kasa. A karamar hukumar ne bataliya ta 23 ta sojin Najeriya ke zaune dirshan, hakan yasa nake kira gare ta da ta tashi tsaye wurin shawo kan matsalar nan.

"Har yanzu ba mu san nufin 'yan awaren ba, ko suna son fadada iyakarsu ko kuma suna son kwace kudu maso yammacin Kamaru kadai

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN