Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya


Labari da dumi da muke samu na cewa, shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu yana da shekaru 73, Khaleej Times ta ruwaito.

Wata sanarwar da kamfanin dillacin labarai ta WAM ta yada a Twitter ta ce:

"Ma'aikatar Harkokin Shugaban Kasa ta sanar da cewa za a yi zaman makoki na kwanaki 40 a hukumance tare da sauke tutoci da kuma rufe ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matakin tarayya da na kananan hukumomi da kuma kamfanoni masu zaman kansu

Sheikh Khalifa, wanda yasha fama da rashin lafiya tsawon shekaru da dama, ya dade da daina shiga harkokin yau da kullum, tare da dan uwansa, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, wanda ake ganin shi ne ke tafiyar da mulki.

Kawo yanzu dai babu sanarwar magajinsa .

Sheikh Khalifa, wanda ba kasafai ake ganinsa a hotuna da wuraren taron jama'a tsawon shekaru, ya gaji mahaifinsa ne kuma wanda ya kafa Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Zayed a shekara ta 2004.

Ya yi fama da bugun zuciya shekaru goma bayan zama shugaba, wanda ya sa ba a ganinsa a bainar jama'a tun daga lokacin.

Hasumiya mafi tsayi a duniya a Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira Burj Khalifa tana daukar sunan marigayin ne, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN