A safiyar yau ne shugaba Buhari ya gudanar da wani zama na ban kwana ga ministocin da suka bar majalisar ministocinsa domin neman mukaman zabe a zaben 2023 mai zuwa.
A wajen taron valedictory wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke Abuja, Shugaba Buhari ya gode wa ministocin bisa hadin kan da suka ba shi, yayin da ya hori sauran mambobin majalisar da su kara himma da jajircewa wajen samun nasarar gwamnatin.
Wadanda suka halarci taron sun hada da karamin ministan ma’adinai da karafa Uche Ogar; Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva; Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige; Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Ministar harkokin mata Pauline Tallen.
Sauran sun hada da ministan harkokin Neja Delta, Goodwill Akpabio; Ministan shari'a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami da ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu.
Mutane tara sun kasance a jiki yayin da tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, wanda shi ne na goma wanda bai sami halartar taron ba amma da dalili .