Yanzu yanzu: Buhari ya umurci mambobin FEC masu burin siyasa su yi murabusShugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci daukacin mambobin majalisar zartaswar tarayya (FEC) da ke neman mukamai na takarar zabe su mika wasikunsu na murabus daga aiki ko kuma kafin ranar Litinin 16 ga watan Mayu, 2022. Gidan talabijin na channels ta ruwaito.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Wadanda abin ya shafa sun hada da ministocin shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami, sufuri, Rotimi Amaechi; Niger Delta, Godswill Akpabio; Ayyuka, Chris Ngige; Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira, Ogbonnaya Onu; Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, wanda ya shiga takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Sauran sun hada da karamar ministar ma’adinai da karafa, Uche Ogar, mai neman kujerar gwamna a jihar Abia, da kuma ministar harkokin mata, Pauline Tallen, wadda ta bayyana burinta na tsayawa takarar kujerar sanata a jihar Filato.

Mista Mohammed ya jaddada cewa wannan wa'adin bai hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ba saboda shi zababben dan majalisar ne.

Ya tabbatar da cewa duk wani gyara ko kari a cikin wannan umarnin za a yada shi daidai.

Ministan ya kara da cewa idan bukatar hakan ta taso, umarnin zai iya hada da wadanda aka nada a siyasance.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN