Da Dumi: Kotu ta umarci a kama AIG na yan sanda da wani Jami'i, duba dalili


Babbar Kotun jihar Ogun ta ba da umarnin tsare mataimakin Sufeta Janar na yan sanda, hedkwatar shiyya ta 2, Onikan, jihar Legas da kuma Sufurtanda, Tijani Taofiq, bisa raina Kotu.

Manyan jami'an yan sandan sun yi watsi da umarnin Kotu wanda ya bukaci AIG ya biya N500,000 yayin da Sufurtanda Taofiq zai biya N50,000 na diyyar ɓata sunan da suka yi wa wani ɗan China, Chen Zheng.

Punch ta rahoto cewa jami'an sun damƙe ɗan China bisa zargin aikata babban laifi kuma daga bisani suka kwace Fasfo ɗinsa.

Mai Shari'a Olugboyega Ogunfowora na babbar Kotun Ogun ya umarci a cigaba da tsare jami'an a gidan Yarin Ibara da ke Abeokuta har sai kayyakin ɗan Chana sun dawo.

A hukuncin da ya yanke ranar 9 ga watan Mayu, Alkalin ya umarci a saki Fasfon mutumin mai lamba No.EB4555829.

Ogunfowora ya yi gargaɗin cewa rashin umarnin Kotu na sakin Fasfon da kuma biyan tarar da aka wa Jami'an raini ne kuma laifi ne da ke kunshe da hukunci a kundin mulkin ƙasa.

Na tsawon yaushe za'a tsare yan sandan?

Ku saurari karin bayani...

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN