Yadda saurayi ya nutse ya mutu yayin ninkaya a cikin kogi


Wani matashi da ake kyautata zaton dan shekara 17 ne, mai suna Abdulkadir, ya nutse yayin da yake  ninkaya a cikin kogi a jihar Kwara.

Lamarin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro a ranar Asabar, ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis a kauyen Ora, Monasara, a karamar hukumar Ifelodun, a jihar inda ya je rubuta jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE).

A cewar wata majiya daga kauyen, “Abdulkabir ya roki daya daga cikin mazauna unguwar mai suna Tosho mai shekaru 10 da abokinsa da su kai shi rafi don yin iyo.

“A kan hanyarsu ta zuwa ne suka hadu da daya daga cikin malaman makarantar wanda ya tambayi inda za su, sai suka yi masa karya cewa za su sayi biredi. Amma a karshe ya mutu.

An tattaro cewa mahaifinsa, Mista Abdulsalam, wanda ke zaune a unguwar Idi-Ape a Ilorin, ya amince a binne shi a bakin kogi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi (SP), da aka tuntube shi ya ce ba a yi masa bayani ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN