Yadda ta faru: Jama'a sun ci karfin jami'an DSS da suka yi kokarin ceto Deborah Samuel - Gwamna Tambuwal


Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya ce an kashe Deborah Samuel dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari ne bayan da wasu gungun matasa suka ci karfin jami’an tsaro da ke makarantar.  LIB ta ruwaito.

Da yake magana a wani taron siyasa a jihar Delta a ranar Asabar, 20 ga watan Mayu, Gwamna Tambuwal ya ce sabanin ra’ayi na gaba daya jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun yi kokarin ceto dalibar Shehu Shagari mai mataki 200 a Kwalejin Ilimin.

“Sabanin yadda kuke tunani, jami’an tsaro musamman DSS, sun samu damar zuwa makarantar a kan lokaci, kuma sun samu nasarar kubutar da Deborah daga hannun matasan da farko.

A yayin da suke tattaro dakaru daga barikin sojoji da, rundunar ‘yan sanda, taron matasan na karuwa. A yayin da muke magana, daya daga cikin jami’an DSS da suka yi yunkurin ceto rayuwarta na kwance a asibiti da bayan an yi masa raunuka a kai, dayan kuma ya samu karyewar hannu.

A zahiri an rinjaye su. Ba kamar an bar ta da kanta ba. Jami’an DSS ne suka ceto ta kuma suna kusa da inda aka kulle ta a dakin masu gadin makarantar, domin sun yi kokarin ceto ta da gaske amma matasan sun ci karfinsu.” Inji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa rikicin da ya barke bayan kashe-kashen ya lafa, kuma jihar Sokoto tana nan lafiya.

An kashe Deborah tare da kona gawarta bayan ta yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad a rukuninsu na Whatsapp.

Tuni dai aka binne Deborah a garinsu na jihar Neja. Rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan ta, sannan ta kuma bayyana cewa tana neman wasu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN