Ana zaman dar-dar a Bauchi sakamakon zargin furta kalaman batanci ga Annabi (SAW) da wata Mrs Roda Jatau ta yi, wanda aka yada a wani dandalin Whatsapp, rahoton Vanguard.
A cewar majiyar, Mrs Jatau ma'aikaciya ce a Hukumar Lafiya Bai Daya ta Jihar Bauchi kuma asalin ta yar Gombe ne amma ta auri wani dan karamar hukumar Warji.
Rahotanni sun nuna cewa matasa musulmi sun bazama nemen matar bayan sallar Juma'a amma ba su ganta ba domin an tsere da ita.
Bayan haka, matasan sun fusata suna ta lalata kayayyaki mallakar kiristoci a unguwar har sun kona wasu gidaje.
Saurari karin bayani ....
Rubuta ra ayin ka