Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni


Shugaban Cocin Methodist, Samuel Uche, a ranar Talata ya ce an biya Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin 'yan bindiga su sake shi, Channels Tv ruwaito.

A wani taron manema labarai a Legas, malamin ya ce an shirya kudaden ne a buhu biyar na Naira miliyan 20 kowanne, kuma Cocin Methodist a Najeriya ne ya tara kudaden.

Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ko ta jiha, ko sojoji ko ‘yan sanda ba su shiga tsakani ba a lamarin

An yi garkuwa da malamin ne a ranar Lahadi a jihar Abia amma a ranar Litinin aka sake shi.

An yi garkuwa da shugaban cocin ne tare da wasu mutum biyu, Bishop na cocin Methodist da ke Owerri da kuma na'ibinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi dauke su ne da misalin karfe biyu na rana a kan hanyarsu ta zuwa wani shirin coci a Okigwe ta jihar Imo zuwa Isuochi a karamar hukumar Umu Nneochi a jihar Abia.

Satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya, ciki har da yankin Kudu maso Gabas inda aka fi dora laifin ta'addanci kan kungiyar IPOB, mai neman ballewa daga Najeriya.

A halin da ake ciki dai, gwamnatin tarayya ta dau mataki mai tsauri kan batun biyan kudin fansa. Kwanan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta biyan kudin fansa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN