Wurare biyar da ke saurin yin wari a jikin dan Adam - isyaku.com NewsBBC Hausa ta ruwaito cewa warin jiki sanannen abu ne da ke shafar ingancin rayuwar mutum. Kuma masana sun bayyana cewa hakan na faruwa ne saboda wasu matakai daban-daban na yaduwar kwayoyin cuta na bakteriya a cikin gumi ko zufa, amma ba saboda ita kanta zufar ba.

Masanan sun kuma yi nuni da cewa akwai rashin fahimtar da ta zama ruwan-dare cewa zufa ko gumi shi ya ke haddasa warin jiki. Amma a kashin gaskiya zufar jikin dan adam ba ta da wari ko kadan.

Jiki kan fitar da wari a baki da sauran sassa, har ma da ruwan jiki. Amma kuma a wannan makalar za mu fi mayar da hankali ne a kan warin da ke fita daga fatar jikin mutum da kuma yanayin yadda kwayoyin cuta na bakteriya ke sarrafuwa a cikin zufa ko gumin dan adam.

Abubuwan da ke haddasa warin jiki

Mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya Medical News Today ta ruwaito cewa galibin warin jiki kan bayyana a fili lokacin shekarun balaga, a yayin da kwayoyin halitta da kuma hanyoyin fitar da zufa suka kara bayyana a lokacin balaga, yayin da sinadaran kwayoyin halittar dan adam da ma'ajiyar zufa ke kara aiki sosai a jikin dan adam.

Kazalika masu kiba da kuma daidaikun mutane masu wasu matsaloli na kiwon lafiya kamar ciwon suga sun fi saukin samun matsalar warin jiki.

Warin jiki na faruwa ne a lokacin da kwayar cuta ta bakteriya ke bin matakai daban-daban na sarrafawa da rarraba kwayoyin halittar sinadarin protein a cikin zufa, inda takan samu abinci - da a sakamakon haka yake fitar da warin.

A cewar Dakta Abubakar Mohammed na Asibitin Kwararru da ke Maiduguri Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, ita kanta zufa ba ita ce ke dauke da wari ba, amma kwayoyin cuta na bakteriya ne da ke samun muhalli a wurin da yake da damshi a jikin dan adam ke sauya zufar zuwa sinadarin asid da kan haddasa warin.

Hakan ne ma ya sa sa in ji shi galibi mutanen da suka fi yin zufa kan fi saurin fuskantar warin jiki.

"Akwai wurare da dama da ba sa shan iska sosai a jikin dan adama, ko kuma wasu luguna a jikin fata musamman wadanda ke da taiba, a nan ne ake samun wurin da zufa ko gumi kan zauna ya dade, don haka kwayar bakteriya kan fake a nan," in ji Dakta Abubakar.

Ya kara da cewa: "Jikin dan adam kan fitar da wasu sinadarai da ke dauke da wari da ake kira odorants, akasarin wadannan na da muhimmanci ga yanayin ayyukan jiki, kuma adadi kadan ba ya haifar da wari mai tayar da hankali."

Amma in ji likitan, idan wadannan sinadaran suka tattaru da yawa a jikin fata sukan sa a rika jin wari.

Har ila yau ya kara da cewa yanayin abincin da mutum ke ci shi ma yana iya sauyawa da kuma kara yawan yanayin warin jikin mutum.

Ya ce: "Cin tafarnuwa, ko albasa ko barkono da makamantansu kan sa zufar da mutum ke fitar wa kara yin wari. Kana idan mutum na yawan cin abinci mai dauke da sinadarin protein ka iya shafar warin jikinsu."

Wuraren da suka fi wari a jikin dan adam

Jikin dan adam na da bangarori da lunguna da matse-matsin da dama da ba sa shan iska.

Kamar yadda mujallar Medical News Today ta wallafa bayanan kwararrun, galibi irin wadannan wurare a jikin dan adama, sun fi zama muhalli ko kuma matattarar kwayar bakteriya inda take samun sukunin rayuwa da kuma yaduwa saboda a duk inda yake da damshi ne take bukata.

Don haka mazaunin gumi ko zufar da ba ta saurin bushewa nan ne inda aka fi samun matsalar fitar da wari a jikin mutum.

Irin wadannan wurare in ji mujallar sun hada da:

Hanyoyin rigakafi da kuma magance warin jiki

Galibi mutane kan fuskanci warin a wasu sassan jikinsa da tufafi ke rufewa kamar - wanda ke kara haifarwa da ajiye damshi da zufa a cikin tufafin wanda ke janyo yaduwar kwayar bakteriya in ji Dakta Abubakar.

Kuma in ji shi ko shakka babu, wannan hanya ce mafi saurin haifar da warin jiki.

"Domin yin rigakafin game da hakan, akwai bukatar kulawa ta musamman a irin wadannan wurare lokacin wanka don tabbatar da cewa sun bushe sosai kafin saka tufafi masu tsafta," in ji shi.

Duk da cewa masana ba su bayyana takamaimen magancewa ko rigakafin abubuwan da ke haddasa warin jiki na bai-daya ba, amma kuma sun bayar da shawarwari na irin matakan da suka kamata a dauka don ragewa ko kashe warin jikin kamar haka:

- Wanka: Ya kamata mutum ya rika yawan wanka da ruwa mai tsafta da sabulu mai kamshi da kuma tabbatar da cewa an goge jikinsu sosai. Kana wanka kamar sau biyu ko uku a rana ita ce hanya mafi inganci - a kuma rika mayar da hankali wajen wanke lunguna da matse-matsin jiki da ke janyo wari kamar hammata da makamantansu.

- Tufafi masu tsafta: Baya ga wanka da tsaftace jiki, yana kuma da matukar muhimmanci ya rika saka tufafi masu tsafta wato wankakku - saboda duk wankan da mutum zai yi muddin tufafin da yake sanyawa na da datti, musamman na wanda ake sakawa daga ciki kamar su kamfai da singileti ko shimi da dan tofi ko siket da rigar mama - to ba zai rabu da warin jiki ba.

- Aski: Barin gashi a wurare kamar su hammata ka iya hana bushewar gumi ko zufa da sauri, da kan bai wa kwayoyin cuta na bacteria damar sakin sinadaran odorants masu sakin wari. Don haka yin aski na taimakawa wajen rage wari a wurin. Za a iya amfani da rezar aski, ko man aske gashi da akan samu a kananan da manyan shaguna.

- Yawan amfani da turaren jiki: yana da matukar muhimmanci a rika yawan amfani da turare na jiki da na gogawa da fesawa a hammata da wasu lungunan jiki, har ma da na tufafi na magance warin jiki.

Karin haske

Baya ga likitoci akwai kuma wasu kwararru a fannin kula da lafiyar jiki a gargajiyance da suka bayyana hanyoyin da suka ce mafiya sauki ne na magance warin jikin kamar:

- Ruwan lemon tsami: amfani da ruwan lemon tsami yana kawar da warin kashi ko jiki, ga misally, idan aka yanka lemon tsamin za a iya gogawa a hammata da duk wasu lunguna da matse-matsin da ke ajiye wari musamman ma idan aka yi zufa kafin a shiga wanka zai kawar warin.

- Sinadarin alum: Musamman idan warin jiki ya yi tsanani, amfani da alum na da matukar muhimmanci saboda karfin da yake da shi wajen kawar da wari da kashe kwayoyin cuta. Idan dan aka zuba alum kadan din a cikin uwan wanka kafin ka yi wanka zai magance warin jiki.

-Ruwan turare da na rose: ruwan wardi ko kuma Rose Water shi ma yana da amfani sosai wajen kawar da warin jiki, kuma akan diga shi a cikin ruwan wanka, yana kuma kara wa jiki kamshi. Akwai kuma turaruka na musamman da a kan diga a cikin ruwan wanka don magance warin jikin.

Wanka sosai, da amfani da turarukan jiki masu tsotse zufa, da kuma aski na taimakawa wajen kawar da warin jiki a cewar Dakta Abubakar.

Sai dai ya ce muddin warin ya wuce misali ya kamata mutum ya tuntubi likita saboda akwai yiwuwar wasu cututtuka ne da ke haddasa fitar wari daga jikin mutum.

"Warin jiki da yawan zufa ka iya kasancewa wata alama ce ta wasu cututtuka kamar su diabetes ko ciwon suga, da ciwon koda da makamantansu, don haka ya kamata mutum ya kula da hakan ya je ya ga likita," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN