Da dumi-dumi: Jami'in Kwastam ya shara wa hadimin Gwamna mari ya ce shi waye (Bidiyo)



Wani faifan bidiyo na wani jami'in kwastam na Najeriya yana marin wani ma'aikacin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya shiga yanar gizo.

Wani dan rajin kare hakkin bil’adama, Harrison Gwamnishu, ya raba bidiyon a daidai lokacin da jami’in kwastan ya mari Mista Samson Nwachukwu a kan babbar hanyar Benin/Agbor a ranar Asabar, 7 ga Afrilu, a gaban abokin aikinsa da wani jami’in soja. 

A cikin faifan bidiyon, ana iya jin jami'in Kwastam din a fusace yana tambayar wanene Mista Samson Nwachukwu bayan ya shaida masa cewa shi mataimaki na musamman ne ga Gwamnan jihar Delta kafin ya yi masa mari. Bidiyon ya kare inda jami'in sojan ya shaidawa jami'in kwastam cewa "ka saukar da mutumin nan."

Ko da yake, Gwamnishu bai bayyana abin da ya kai ga marin ba, amma ya sha alwashin neman a yi adalci a madadin Mista Nwachukwu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN