Type Here to Get Search Results !

An raunata Fasto, an kona gidaje yayin da wasu fusatattun matasa Musulmi ke neman wata mata da ta zagi Annabi a Bauchi (bidiyo)


An raunata wani Fasto tare da kona gidaje da dama yayin da wasu fusatattun matasa Musulmi suka je neman wata mata da ta aikata sabo a jihar Bauchi.

An ce matar ta watsa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta inda wani da ya Musulunta ya yi magana kan Annabin Musulunci.

Matar da ake magana a kai ma’aikaciyar gwamnati ce ’yar asalin Gombe, amma ta yi aure a karamar hukumar Warji da ke Bauchi.

Wasu fusatattun matasa ne suka je neman matar bayan sallar Juma’a a ranar Juma’a 20 ga watan Mayu, inda ba a same ta ba, sai dai ana zargin cewa sun kai farmaki inda suka lalata kadarori na mabiya addinin Kirista a yankin Katangan da ke karamar hukumar Warji a jihar Bauchi. .

Wasu Kiristoci da suka hada da wani Fasto na Cocin ECWA, sun jikkata.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan da Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, ta gamu da ajalinta bayan ta zagi Annabi Muhammad (SAW).

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies