Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Keffi, Muhammad Shehu, tare da direbansa.
An sace shi ne a daren Juma’a, 20 ga watan Mayu, yayin da yake tafiya tare da direbansa da ‘yan sanda cikin tsari.
An ce ‘yan bindigar sun tare shingayen titin Keffi zuwa Akwanga inda suka yi ta harbe-harbe ta iska wanda hakan ya tilasta musu tsayar da motar da suke ciki kafin a yi garkuwa da su.
A kokarin ganin an shawo kan lamarin, dogarinsa na ‘yan sanda ya yi kokarin dakile harin amma abin takaici ya rasa ransa a cikin lamarin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda sun karbe inda aka kai harin domin ceto wadanda lamarin ya shafa tare da kamo masu garkuwa da mutane.
Yace;
“Yanzu haka jami’an ‘yan sanda suna yankin da aka yi garkuwa da su. Mun karbe muhalli kuma ina tabbatar muku nan ba da dadewa ba za a kubutar da su kuma wadanda suka aikata wannan aika aika ba za su tsira ba.".
Rubuta ra ayin ka