Tambuwal: Buhari ya nunawa mutanen kudu maso gabas son kai a gwamnatinsa


Gwamnan jihar Sokoto kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa zai tafiyar da gwamnati wacce za ta dama da kowa idan aka zabe shi. 

Da yake magana da mambobin jam’iyyar a Imo a ranar Juma’a, Tambuwal ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ‘ragi’ yankin kudu maso gabas ta hanyar kin nada mutanen yankin a manyan mukaman gwamnati, jaridar The Cable ta rahoto.

Gwamnan ya bayyana cewa mutanen yankin suna ganin an mayar da su saniyar ware a gwamnatin Buhari.

Daily Post ta nakalto Tambuwal yana cewa:

“Buhari ya ragi yankin kudu maso gabas. Ni ne na shawarci Saraki da ya zabi Ekweremadu domin zama mataimakinsa a 2015. Akwai lamari na mayar da mutanen kudu maso gabas saniyar ware.

“Shugabannin manyan hukumomin gwamnati guda goma ba yan kudu maso gabas bane, ciki harda gwamnan CBN.

“Babu ko daya daga cikin shugabannin tsaro da ya fito daga kudu maso gabas. Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, mataimakin shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa duk ba yan kudu maso gabas bane. A karkashin kulawata hakan ba zai taba faruwa ba. Za a dama da kowani yanki na kasar nan.”

Yayin da yake bayyana mutanen kudu maso gabas a matsayin masu kasuwanci, Tambuwal ya ce za a nada su a mukamai masu muhimmanci idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

“Ba za a iya ware yankin kudu maso gabas da musamman jihar Imo ba. PDP za ta kwato Imo idan na zama shugaban kasa. Mutanen Igbo sun san kan kasuwanci. Za ku same ni a matsayin abokin tarayya.

“Muna aiki tare da yan uwanmu a Sokoto. Mun dawo da zaman lafiya yanzu a jihar Sokoto. Zan kasance shugaban kasa ga dukkan yan Najeriya.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN