Batanci: CAN ta canza fasalin zanga-zangar da ta shirya yau kan kisan DeborahƘungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) ta bukaci kiristoci su canza dabarar zang-zanagar kashe Deborah Samuel a Sakkwato bisa zargin ta zagi Annabi SAW a Sokoto.

Shugaban CAN na ƙasa, Dakta Samson Olasupo Ayokunle, shi ne ya sanar da sabon canjin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya umarci dukkanin shugabannin Coci Coci da wuraren ibadar mabiya addinin Kirista da su gusdanar da zanga-zangar lumana a cikin Cocin su a yau Lahadi, 22 ga watan Mayu, 2022.

Sanarwan ta ce:

"Duk kuna da masaniyar cewa wasu Musulmai sun fitar da bayanan zasu kalubalanci zanga-zangar lumana da muka shirya ranar Lahadi 22 ga Mayu."

"Manufar su shi ne su tada zaune tsaye kuma su jingina mana laifin, saboda haka ina rokon ku baki ɗaya ku yi zanga-zanga ɗauke da alluna a ciki harabar Coci Cocin ku ko Sakatariyar CAN."

"Idan hakan ba ta samu ba, ku yi a cikin Coci ku ɗaga alluna ku yi Addu'a a yi wa Deborah Samuel Adalci. Ku yi Addu'a Allah ya canza cuciyar wanda ke da nufin kashe mutum ɗan uwans ada rigar addini.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN