Wani magidanci da masoyinsa sun mutu yayin da suke lalata a cikin mota ana shagalin Sallah


An tsinci gawar wani magidanci da masoyinsa da suke jima'i a cikin wata mota kirar Sports Utility (SUV) a Estate Jakande dake Isolo a Legas. 

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa makwabta sun gano cewa masoyn sun mutu ne a ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, bayan da suka lura cewa motar ta kasance cikin daren Asabar 30 ga Afrilu. 

An bayyana sunan mutumin mai suna Koyejo kuma an ce ya dauko masoyiyarsa ne a Isolo a lokacin da ya nufi gidansu da ke Estate Jakande.

An gano cewa mutumin Injiniyan IT ne wanda ke zaune da matarsa ​​a Surulere, rahotanni sun bayyana cewa ya kira abokansa ya shaida musu cewa yana nan kusa, sannan ya siya suya kafin ya tsayar da motarsa amahadar Double Star domin yin nishadi a cikin motar.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa, sun fara shakka ne bayan gano cewa motarsa ​​mai lamba EPE666GE, tana wajen duk tsawon daren Asabar zuwa daren Lahadi kuma a wuri guda. 

Majiyar ta ce; 

“A lokacin da suka suka kunna tocila sun ga Koyejo, tsohon mutuminmu ne. Amma ba mu san ko wacece yarinyar ba.

“A yammacin yau ne aka ce mana ya je ya dauko yarinyar a Isolo. Suya suka siya a tashar Moshalashi. Wani abu ya kai ga wani kuma suka fara soyayya a cikin mota.

“Ba wanda ya san abin da ya kashe su. Koyejo yana tsirara yayin da yarinyar ta zazzalo wandonta ne.

“Daya daga cikin mutanen yankinmu ya Kira matar Koyejo da ke zaune a Surulere. Ta ce tun ranar Asabar ba ta iya samun mijin nata ba wayarsa a kashe.

“Sai da muka tuntubi ‘yan sanda a Ejigbo da suka zo suka tafi da su da mota. Jikin Koyejo ya fara barewa. Hancin yarinyar yana fitar da jini.

“Babu wani rauni a jikinsu. 'Yan sanda ne kawai za su iya ba da labarin abin da ya faru kafin su mutu. An kai gawakinsu babban asibitin Isolo.” 

Kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa binciken kimiyya kan gawarwakin mutanen ne kawai zai iya bayyana musabbabin mutuwarsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN