Eid: Shugaba Buhari yace ba ya iya bacci saboda halin da Yan Najeriya ke ciki


Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya haɗu da sauran yan uwa musulmai a filin Fareti na Barikin sojojin Mambila domin gudanar da Sallar Eid-El-Fitr wato ƙaramar Sallah.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa shugaban kasan, tare da wasu daga cikin iyalansa da hadimansa sun isa wurin Idi da misalin ƙarfe 9:00 na safiya.

Sauran mutanen da suka halarci Masallacin idin sun haÉ—a da mambobin majalisar zartarwa, hafsoshin tsaro, shugabannin hukumomin tsaro da wasu jiga-jigan gwamnati, Premium times ta ruwaito.

An gudanar da Sallar Idi mai Raka'a biyu bisa jagorancin Limamin Barikin, Muhammad Dahey-Shuwa, wanda ya yi nasiha kan muhimmanci da darussan watan da ya gabata wato Ramadan.

A huɗubar da limamin ya gabatar, ya yi addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan, inda ya bukaci mutane su cigaba da kai kukansu ga Allah kuma su taimaka wa jami'an tsaro.

Jawabin Buhari bayan kammala Sallah

Yayin amsa tambayoyi bayan kammala ibadar Sallah Eid, Buhari ya ce baya iya bacci da dare saboda rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar nan.

Ya kuma yi alƙawarin cewar ba zai gajiya ba wajen jajircewa a kokarin kawo ƙarshen dukkan ƙungiyoyin yan ta'adda.

Dangane da zaɓen 2023 dake tafe, Buhari ya ƙara jaddada shirin gwamnatinsa na tabbatar da an gudanar da ingantace kuma sahihin zaɓe babu ɓoye-ɓoye.

A gaba ɗaya watan Azumin Ramadana, Shugaba Buhari ya kasance yana halartar Masallacin fadar shugaban kasa wajen Tafsirin Alƙur'ani mai girma.

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa daga N30,000 da gwamnatin tarayya ta ƙayyade zuwa N40,000.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana wannan ƙarin ne yayin taya ma'aikata murnar 'Ranar ma'aikata ta duniya' ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN