Akwai manyan alamu da ke nuna cewa gwamnatin tarayya na iya biyan bukatun 'yan ta'addan da suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna farmaki inda suka sace sama da fasinjoji 68 a Katari, jihar Kaduna a ranar 28 Maris.
Kungiyar 'yan ta'addan ta bukaci a sako wasu daga cikin kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu sannan su sako wadanda suka yi garkuwa da su, jaridar Punch ta ruwaito.
A kalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 26 suka jigata yayin da 'yan bindiga suka saka bam a layin dogon kuma suka fara harbe-harbe kan jirgin da ke tafiya zuwa Kaduna.
'Yan bindigan sun sako wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su. Daga ciki akwai manajan daraktan BOA, Alwan Hassan, Sadiq Ango Abdullahi, dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi.
The Punch a ranar Lahadi ta gano cewa, sasanci tsakanin 'yan ta'addan da gwamnati yana cigaba. A farko gwamnatin ta fara tunanin ko ta kai farmakin karar da kowa a sansanin ne, wanda hakan ke da hatsari.
A ranar Laraba da ta gabata ne 'yan bindigan suka saki hoton jaririya mace wacce daya daga cikin matan da ke hannunsu mai juna biyu ta haifa.
An sakankace cewa sun saki hoton jaririyar ne saboda su nuna wa duniya cewa jaririyar tana cikin koshin lafiya wanda hakan zai karfafa guiwar masu sasanci da su.
Majiyoyin tsaro sun ce 'yan bindigan sun dage kan cewa sai dai a sako mambobinsu da ke hannun hukuma tare da basu wasu kudi masu nauyi kafin su saki wadanda suka sace da suka hada da kananan yara, mata da magidantan maza.
"Sasancin da ake yi tsakanin 'yan ta'adda da gwamnati yana tafiya, amma gwamnati na duba yadda za ta karbo jama'a ne ba tare da an samu tangarda ba.
"'Yan bindigan na son a saki kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu, suna kuma son kudi makudai. Ana sasancin da su ta yadda ba za a yi karantsaye ga tsaron kasa ba ko kuma lafiyar wadanda aka sace," majiyar tace.
Harin ya faru ne a 28 ga watan Maris a dajin Dutse cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wanda ya lashe rayukan mutane takwas, tare da raunata wasu 26 bayan fasinjoji da dama da suka bace - wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da su.
Channels Tv ta ruwaito cewa, bayan sati biyu da batan su, iyalansu na sa ran za su samu 'yanci daga garkuwan da aka yi dasu, duk da sun ki amincewa da neman sasanci da 'yan bindigan.