Tashin hankali: Yan bindiga kimanin 200 kan babura sun farmaki Katsina sun tafka mumunar barna

 


Wasu yan bindigan daji sun farmaki shingen binciken jami'an tsaro da ke Mil Takwas, yankin Jibiya, wanda ba shi da nisa sosai zuwa cikin birnin Katsina.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa Gomman yan bindigan sun fito ne daga yankin Bugaje, amma wani ɗan Acaɓa ya ankarar da jami'an tsaron da ke Shingen game da motsin maharan.

Ya ce wasu dakarun sojoji suna wurin mintuna 30 kafin harin, sun bar wurin ne bayan samun rahoton gaggawa cewa wasu mahara sun nufi wani gati daga ƙauyen Tsambe.

Ya ce:

"An samu bayanan sirri na motsin yan bindigan daga Bugaje saboda wasu sojoji na wurin domin gwabzawa, amma sai sojoji suka samu wani rahoton wasu gomman yan bindiga sun nufi Jibiya daga Tsambe, hakan yasa suka tafi tarar su."

"Bayan Mintuna 30 wani ɗan Acaɓa ya gaya wa Dakarun tsaron da ke wurin cewa yan bindiga sun nufo wajen Shingen, kuma bisa rashin sa'a kaɗan ke da bindiga dan haka suka tsere, maharan suka zo suka kone motoci uku."

Mutum nawa harin ya shafa?

BBC Hausa ta ruwaito cewa maharan haye kan babura sama da 200 sun farwa shingen binciken ababen hawa na Jami'an Kwastam, inda suka ƙona motoci hudu.

Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce harin ya faru da tsakar daren ranar Lahadi, kuma an kashe wani Direban Motar haya amma bai san yadda Fasinjojin motar suka yi ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN