Da dumi-dumi: An yi wa Dan Acaba kisar gilla an gudu da Babur dinsa (Hotuna)

 


Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani dan acaba mai suna Goodnews Okrinya a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Wanda aka kashe wanda aka fi sani da J-Martins daga unguwar Emeyal 2, an kashe shi har lahira kuma an sace masa babur a kan titin Imiringi/Emeyal ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu.  

An tsinci gawar Okrinya a yankin Bakery a unguwar Imiringi a safiyar ranar Litinin, 30 ga Mayu, an tarar da an yanke masa wuya. 

Shugaban karamar hukumar, Cif Ebinyo Marvin Turner, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya bayyana kisan a matsayin rashin hankali da dabbanci, yana mai kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen dakile wannan mummunar dabi’a. 

Ya ba da tabbacin cewa wadanda ke da hannu a wannan aika-aika za a cafke su kuma su fuskanci fushin doka. 

Daga nan sai ya yi kira da a kwantar da hankulan al’ummar yankin, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin majalisarsa tana kan gaba wajen dakile duk wani abu da zai sake faruwa a yankin.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN