Malamin makaranta ya yi wa dalibarshi yar shekara 13 mugun aiki, duba ka gani | isyaku.com


Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani malami dan shekara 25 mai suna Ayobami Oluwatobiloba Runsewe bisa zargin yi wa dalibar sa mai shekaru 13 fyade (an sakaya sunanta).

Wanda ake zargin, malamin aji a makarantar reno da firamare a Ago Iwoye, karamar hukumar Ijebu ta Arewa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta ranar Asabar.

A cewar Oyeyemi, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai hedikwatar Ago Iwoye.

PPRO ta ce mahaifiyar yarinyar ta shaida wa ’yan sanda cewa, wanda ake zargin ya yaudari diyarta zuwa gidansa da ke unguwar Ayegbami a Ago Iwoye bayan kammala karatun makaranta da misalin karfe 4:30 na yamma ya kuma yi lalata da ita.

Ya ce an kawo wandon yarinyar wanda yake joke da jini a matsayin shaida.

“Bayan rahoton, DPO na hedikwatar sashin Ago Iwoye, SP Nuhu Adekanye ya tura jami'ansa  a wurin, inda ba tare da bata lokaci ba aka cafke malamin.

"A kan tambayoyi, da farko wanda ake zargin ya musanta cewa wani hulda ya shiga tsakaninsa da yarinyar, amma lokacin da yarinyar ta fuskance shi, ya kasa cewa komai," in ji PPRO.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa sashin yaki da fataucin bil’adama da aikin yara na sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN