Murna a jihar Kebbi bayan Ministan shari'a Abubakar Malami ya gwangwaje masoyansa da kyautar manyan motoci (Hotuna)Jama'a da dama tare da yan uwasu da abokan arziki sun kaure da farin ciki da murna bayan Ministan shari'a kuma Antoni janar na Najeriya Dr. Abubakar Malami ya gwangwaje su da kyautar manyan motoci ranar Lahadi.

Shafin isyaku.com ya samo cewa irinsa na farko a jihar Kebbi, wanda kyautar ta motoci ne sabbi kuma ajin motoci masu tsada.

Dr Abubakar Malami ya gwangwaje jama'a masu yawan gaske da kyautar kayan Azumin Ramadan, na buhunan shinkafa, gero, da suga. Bayan kyautar abincin tafi da gidanka (Take away) da tsarinsa ya dinga raba wa bayjn Allah a fadin garin Birnin kebbi kullum hat karshen watan Ramadan.

Hotunan kadan daga cikin wasu.motocin da Malami ya bayar kyauta ga masoyansa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN