Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi dan shekara 36 mai suna Bako Anjeh da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 17 fyade har lahira a karamar hukumar Nasarawa-Eggon ta jihar Nasarawa.
Wanda ake zargin wanda ya tilasta wa yarinyar shan gramoxone (wani sinadari da ake amfani da shi wajen kashe ciyayi) domin ya raunatata kafin ya yi mata fyade, an kama shi ne bayan da mahaifin yarinyar, Mista Dimka Sarki ya shigar da kara a ofishin rundunar yan sanda yankin Akwanga.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel ya kuma bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin gaban kuliya bayan kammala bincike a sashin binciken manyan laifuka na jihar dake Lafia.
Nansel ya ce;
“Wani mai suna Dimka Sarki ne ya shigar da kara a rundunar ‘yan sandan yankin Akwanga, cewa wani Bako Anjeh ya yaudari ‘yarsa zuwa dakinsa kuma ya yi kokarin sanin ta ba bisa ka’ida ba. Wanda ake zargin ya fito daga kauyen Angam da ke yankin Raya Akun a karamar hukumar Nasarawa-Eggon.
“Lokacin da ta ki, sai ya ba ta gramoxone da karfi, wani sinadari da ake amfani da shi wajen kashe ciyawa, ta sha, wanda ya sa ta yi rauni a lokacin. Daga bisani ya ci gaba da yi mata fyade. .
“Bayan karbar korafin, jami’an ‘yan sandan da ke yankin Akwanga suka garzaya wurin da lamarin ya faru sannan suka kama wanda ake zargin.
“An kai wacce aka kashen zuwa asibitin Ola da ke karamar hukumar Akwanga domin kula da lafiyarta inda aka dauki bayananta kafin daga bisani ta rasu a wannan asibiti.”