Maciji ya yi wa maigida mugun cizo yayin da yake zaune a tukunyar ban daki, duba yadda ta faru


Wani maciji da ya dade yana kwantan bauna a bandakin wani mutum ya sare sa a mazaunensa yayin da mutumin ke kan tukunyar masai rike da wayarsa yana wasa da ita.

Sabri Tazali, daga kasar Malaysia ya rayu bayan farmakin da macijin ya kai masa, Shafin LIB ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana bayan farmakin da macijin ya kai masa ya yi "sa'a" kasurgumin macijin bai sare sa a al'aurarsa ba.

Yadda macijin ya sari mutumin

Macijin ya sari Tazali, mai shekaru 28 yayin da yake tsaka da amfani da bandaki a gidansa cikin garin Selayang a jihar Selangor dake kasar Malaysia inda yaji wani irin sara mai kaifi a mazaunensa.

Bayan yaji alamar sarar macijin a mazaunensa, Tazali ya yi hanzarin mikewa gami da cafko macijin tare da buga sa da bangon bandakin.

Cikin firgici, daga nan ne ya balle kofar bandakin yayin kokarin budewa cikin hanzari.

Sai dai a sa'ar Tazali, macijin ba mai dafi bane.

Nan take ya garzaya asibitin karamar hukumar don a duba masa ciwon sa tare da samun allurar magani daga likitoci.

Daga bisani, 'yan kwana-kwana suka isa gidan don cire macijin.

Tazali ya bayyana wa kananan jaridu yadda har yanzu yake cikin wani yanayi na firgici bayan farmakin da macijin ya kai masa, hakan yasa ya koma amfani da bandakin masallacin kusa da su na tsawon makwanni biyu a maimakon nasa.

Yayin wallafa bidiyon a kafafan sada zumuntar zamani, ya rubuta: "Wani maciji ya sari mazaunai na. Macijin ya fito ne daga cikin tukunyar masai."

Ya kara da cewa: "Cikin sa a, bai ciji kwayayen haihuwana ba."

Ya cigaba da bayyana yadda cikin firgici ya tumbuko "rabin hakorin macijin" daga mazaunansa inda macijin ya saresa. Ya zargi cewa hakorin ya balle ne yayin da ya "bugi macijin da karfi" gami da jefar da shi jikin bango.

A halin yanzu, Tazali ya canza tukunyar masan mai kalar hanta da dalleliyar sabuwar fara yadda zai iya ganin cikin yadda ya dace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN