Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar arewa


Wasu ‘yan bindiga sun kashe deliget-deliget uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban kwamitin zabe kuma mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Lawrence Ewhrudjakpo ne ya sanar da haka a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar, wurin da aka gudanar da zaben fidda gwanin.

An ce an kashe su ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke komawa Mariga bayan da jam’iyyar ta dage zaben fidda gwanin sakamakon zanga-zangar da wasu ‘yan takara suka yi da nuna rashin amincewa da jerin sunayen wasu deliget din.

Daga nan ne aka bukaci da su kawo shaidan tantance sunayensu don tantance bayanasu a zaben fidda gwanin da aka canja zuwa ranar Alhamis.

An sauya wadanda suka rasa rayukansu a lamarin domin cike adadin deliget daga karamar hukumar.

Sakamakon haka, daya daga cikin deliget din, Shehu Haruna ya shaida wa Daily trust cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Mariga da Tegina kuma mutane hudu sun rasa rayukansu.

A cewarsa:

“Mun bar Minna ne cikin kurarren lokaci bayan da PDP ta dage zaben fidda gwani na gwamna zuwa ranar Alhamis, cewa mu je mu kawo katin zabe ko kuma wata hanyar ta tantance ingancinmu.

“Muna komawa gida ne domin dauko bayananmu, kuma a kan hanya muka ci karo da ‘yan bindigar da suka bude wa motar mu wuta. Ko da yake mun iya tserewa tunda ba a harbi direban ba, amma mutane hudu sun mutu nan take.”

Ya ce karamar hukumar ta su da ke kan iyaka da Birnin-Gwari a Kaduna ta zama maboyar ‘yan bindiga da ke aikata ta’addanci akai-akai.

Haruna ya yi kira da a samar da jami’an tsaro na dindindin a yankin da su kare matafiya da al’ummomin yankin.

Karin bayani na nan tafe..

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN