Karfin hali: Barawo ya tafka satar kudi a caji ofis na yansanda yayin da yake tsare, duba abin da ya faru


Wata kotun unguwar Dei-Dei da ke Abuja, a ranar Litinin, ta yanke wa wani direba mai suna Habib Dada mai shekaru 34 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar N13,250 mallakin wani da ake zargi da ke tsare a hannun ‘yan sanda.

Dada da ke Guzape, a kauyen Asokoro, Abuja, ya amsa laifinsa na tserewa daga hannun jami'ai da kuma aikata sata tare da rokon a yi masa sassauci, rahoton Daily trust.

Sai dai alkalin kotun, mai shari'a Sulyman Ola, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N40,000 a kan tuhume-tuhume biyu, sannan ya gargade shi da ya daina aikata laifiN.

Mai shari'a Ola ya kuma umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya N13,200 da ya sata a ofishin ‘yan sanda, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya sruwaito.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin yana tsare ne a magarkamar ‘yan sanda na Efab Estate ranar 29 ga watan Afrilu, bisa laifin satar kayan motsa jiki, waya iPhone da kuma batirin mota.

Ogada ya ce dan sanda ya fito da mutane biyu da masu laifi, daga nan ne wanda ake zargin ya yi amfani da damarsa wajen fauce kudin tare da tserewa daga magarkamar 'yan sanda.

Mai gabatar da kara ya ce daga baya ‘yan sanda sun gano shi tare da sake damko shi.

A halin da ake ciki, kotun, a wata shari’ar ta daban, ta kuma yanke masa hukuncin daurin wata tara a gidan yari saboda satar kayan motsa jiki mallakin wano uban gidansa.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi da laifin cin amana da sata sannan ya roki kotu da ta yi masa sassauci

Alkalin kotun, Sulyman Ola, ya baiwa Dada zabin biyan tarar N25,000 tare da umartarshi da ya biya N520,000 a matsayin diyya ga wanda ya yiwa asara

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN