Da Duminsa: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar shugaban kasa


Wani rahoto da ke fitowa ya nuna cewa gwamnonin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC sun amince da zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a gudanar kafin babban zaben 2023.

Legit ta ruwaito cewa Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC wanda ya bayyana hakan, ya fadi a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, cewa gwamnonin sun ba da cikakken goyon baya ga duk wani mai neman tsayawa takarar shugaban kasa domin nuna bajintarsa cikin gaskiya da adalci.

Wannan magana dai ta fito ne bayan wata tattaunawa ta sirri da gwamnonin jam’iyyar mai mulki suka yi, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya

"Gwamnonin APC sun bayyana goyon bayansu ga zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a gudanar, tare da baiwa duk wani wanda ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa damar yin takara cikin gaskiya da adalci."

Previous Post Next Post