Da dumi-dumi- An bindige dan sanda har Lahira, an raunata daya sakamakon barkewar rikici a zaben fidda gwani na PDP a jihar Cross River


An harbe wani dan sanda mai suna Martins Mbang a wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Obudu a jihar Cross River.

Zaben fidda gwani shi ne na tsayar da dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 na mazabar tarayya ta Obudu/Obanliku/Bekwara. 

An tattaro cewa an harbe dan sandan da abokin aikinsa a makarantar yara ta Handmaid International Nursery and Primary School inda ake gudanar da zben na fidda gwani.

A cewar Cross Rivers Watch, magoya bayan wasu daga cikin ‘yan takarar sun gudanar da zanga-zangar ne ba tare da sanin wasu dalilai ba inda suka bude wuta kan ‘yan sandan.

An yi ta harbe-harbe da dama na kusan mintuna shida wanda aka ce ya yi tsami. Daga karshe dai an fatattaki ‘yan bindigar yayin da ‘yan jam’iyyar PDP suka tsara yadda za su yi. 

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Irene Ugbo, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Litinin 23 ga watan Mayu, ta ce wani jami’in dan sanda guda ya samu rauni yayin da aka kama mutum takwas. 

“An kashe daya daga cikin jami’an mu, wani kuma ya samu rauni. Mun kama mutane takwas da ake zargi da hannu a lamarin,” in ji PPRO.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN