Kannywood: 'Ni jikan Aminu Kano ne' Jarumi Ali Rabiu Ali ya fito takara a 2023

 


Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Dala ta jihar Kano. Legit.ng ta ruwaito.

A wata Fasta da jarumin da saki a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da Daddy ya nuna cewa yana fatan ya zama magajin Malam Aminu Kano.

Ali wanda Furudusa ne kuma Darakta fim a ya wallafa Hotonsa ɗauke da Fom ɗin takara karkashin inuwar jam'iyyar PRP.

Ya ce ya ɗaɗe yana ciwom yadda ake jagoranci tun daga matakin ƙasa, jihohi. kananan hukumomi da ma'aikatun gwamnati domin shugabanni ba ta talakawa suke ba, manufar kansu kaɗai suka tasa a gaba.

A cewarsa abokanai da yan uwa sun jima suka rokon ya fito takara domin taimaka wa Talata saboda sun san abin da ke cikin zuciyarsa amma yace bai yarda ba ganin ba zai iya shiga cikin yan siyasa ba.

Ni jikan Aminu Kano ne - Ali

Haknan Jatumin ya bayyana cewa shi jikan Malam Aminu Kano ne ksancewar shi ne wanda ya haifi mahaifiyarsa, sai dai a bayaninsa ya ce yan siyasar yanzu sun bar turbar da kakansa ya ɗora su.

Ali ya ce:

"A sani na yan siyasar zamanin nan mafi yawa sun bar kan aƙidar Kakana Malma Aminu Kano ta ɓangaren kokarin kwato hakkin talakawa da rike amana, kula da lafiya, ilimi da walwalar talakawa."

Zan ɗora daga inda kakana ya tsaya

Bayan haka, Dadɗy ya ƙara da cewa ya yi kudirin tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiƙtar Dala mahaifarsa karkashin inuwar PRP da Malam Aminj Kano ya kafa.

"Ina fatan ɗorawa daga inda ya tsaya da yardar Allah kuma da karfin ikon Allah domin na yi bakin kwarkwardo a ɓangaren wakilci. Idan zan zama Alkairi da al'ummar Dala Allah ya sani."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN