Da dumi-dumi: Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi (Bidiyo)


An kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi) 

21st CENTURY CHRONICLE ta ruwaito cewa an kashe dalibar mai suna Deborah bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki. 

Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe. 

Yanzu dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar, riwayar TVCNews. 

An tattaro cewa Deborah ta furta kalaman batancin ne a dakin kwanan dalibai sakamakon rashin jituwan da ya auku tsakaninta da wasu dalibai. 

Daya daga cikin daliban da ta bukaci a sakaye sunanta tace: 

An bukaceta ta janye kalamanta amma ta 'kiya, hakan ya fusata sauran dalibai Musulmai a kwalejin." 

Wata majiya ta bayyana cewa jami'an tsaron makarantar sun boyeta a ofishinsu amma fusatattun matasa suka fi karfinsu, suka kasheta, sannan suka kona gawarta. 

Ance jami'an tsaro yanzu sun mamaye makarantar. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN