Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani


Hukumar jirahen kasan Najeriya NRC ta dakatar da dawowar jirgin kasan dake jigilar fasinjoji tsakanin Abuja da Kaduna sai wani lokaci da ba'a sani ba.

Wannan ya biyo bayan lashe takobin da iyalan wadanda aka sace a jirgin kwanaki suka yi na cewa ba zasu amince jirgin ya dawo aiki ba sai an dawo yan'uwansu da aka sace. 

Kakakin hukumar NRC, Mr. Mahmud Yakub, a jawabin da ya fitar ranar Juma'a ya bayyana cewa za'a sanar da sabon ranar dawowar jirgin 

Yace: 

"Hukumar NRC zata cigaba da bada hadin kai da gwamnatin tarayya wajen kare rayukan mutanen Najeriya da dukiyoyinsu."

 "Hakazalika muna jajantawa iyalan wadanda ke hannun yan bindiga har yanzu sakamakon harin da aka kai jirgi kuma muna tabbatar muku gwamnatin tarayya na kokarin ceto dukkan wadanda ke tsare." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN