Da Dumi-Dumi: Zan zaɓi magaji na a 2023 ku goyi baya na, Buhari ga gwamnonin APC


Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gaya wa gwamnonin APC cewa zai so ya zaɓi wanda zai gaji kujerarsa kuma yana bukatar goyon bayan su yayin hakan.

Shugaba Buhari ya faɗi haka ne a wurin taronsa da gwamnonin jam'iyyar APC ranar Talata da Aso Villa da ke Abuja, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Buhari ya ce:

"Domin cigaba da kyawawan tsarukan da jam'iyyar mu ta kafa yayin da muke fuskantar babban taro nan da yan kwanaki, ina bukatar goyon bayan gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki wajen zaɓo magaji na."

"Wanda zai karɓi turar jam'iyya a zaɓen 2023 har ya samu nasarar shiga ofishin shugaban ƙasa a tarayyan Najeriya a zaben 2023."

Shugaba Buhari ya faɗa wa gwamnonin cewa, "Akwai tarin bukatar ya samar da jagoranci mai ƙarfi a jam'iyya karkashin wannan lamarin na matakan canza gwamnati."

Buhari ya ce gina shugabanci mai ƙarfin ba wai kawai don ya ƙara inganta sa'ar APC a zaɓe kaɗai bane, har da tabbatar wa jam'iyyar ta zarce kan karagar mulki tun daga sama.

Ta yadda zan zaɓi magaji na - Buhari

A taronsa da gwamnonin, shugaban ƙasan ya faɗa musu abubuwan da zai duba kafin ya zaɓi ɗan takarar da zai goya wa baya daga cikin mutum 25 da ke neman tikitin APC.

"Abin da zamu sa a gaba shi ne nasarar jam'iyyar mu kuma ɗan takarar da zamu zaɓa wajibi ya kasance wanda zai ba yan Najeriya natsuwar samun nasara da tabbaci tun kafin zaɓe."

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta soke amfani da 'Fom ɗin abun da ya faru' yayin gudanar da zaɓe a faɗin Najeriya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Talata 31 ga watan Maris, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN