2023: Buhari ya fadi mutumin da zai mika wa mulki


Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara matsowa kusa, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake magana kan mutumin da zai gaje shi bayan wa'adinsa ya ƙare.

Daily Trust ta rahoto cewa a shekarar da ta gabata lokacin da ya zanta da wata kafar Talabijin a Najeriya, shugaba Buhari ya ce bai damu da ko waye zai gaji kujerarsa ba.

Daga bisa kuma shugaban ya ce duk da yana da wanda yake son ya gaje shi a zuciyarsa, amma ba ya son ya bayyana wa duniya shi saboda, "da yuwuwar a kawar da shi idan ya faÉ—a."

Sai ɗai da yake jawabi bayan kammala Sallar Idin ƙaramar Sallah a Barikin Mambila dake Abuja, Buhari ya jaddada cewa jajircewar da gwamnatinsa ke yi na tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.

Da aka tambaye shi kan wanda yake son ya miƙa wa mulki a 2023, Shugaba Buhari ya ce: "Mutumin da yan Najeriya suka zaɓa."

Shugaba Buhari ya umarci Hafsoshin tsaro

Bayan haka shugaban Buhari ya ƙalubalanci hafsoshin tsaro da dukkan hukumomin tsaron ƙasar nan su bi yan ta'adda har maɓoya su kawar da su daga duniya.

Buhari ya jaddada manufar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya.

Ya ƙara da cewa wajibi a tabbatar da tsaron manoma yayin da suke gab da komawa gona, domin ceto ɓamgaren samar da abincin ƙasar nan.

"Zmau cigaba da samar da tsaro musamman lokacin da muke fuskantar damina, sabosa manoma su koma gonakin su, har Allah ya sa mu fita daga hatsarin tsaron abinci."

"Shugabannin dakarun tsaro; Sojojin ƙasa, Sojojin ruwa, sojojin sama, Sufetan yan sanda da sauran makamantansu sun san halin da ake ciki sarai. Haƙƙin su ne binciko inda yan ta'adda suke kuma su sheƙe su."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN