Dan kwaya ya kutsa Fadar Sarki ya kwamushe hakorin Basarake tare da aikata barna


Fadar Soun Ogbomoso ta tabbatar da cewa wani magidanci mai suna Bukola Adediji mai shekaru 30 da aka fi sani da Ajanlekoko ya kutsa kai tare da lalata wasu kadarori cikin Fadar.

Mutumin da ake zargin dan shaye-shayen miyagun kwayoyi ne, kuma ake zargin ba shi da hankali, an bayyana cewa, ya kai hari kan daya daga cikin sarakunan da suka yi kokarin hana shi shiga cikin dakin zama tare da kwamushe hakoran wani basarake a lokacin harin.

Ya kuma lalata wasu kofofi a fadar kafin wasu mutane su yi galaba a kansu, suka dunkule shi kuma suka fitar da shi daga Fadar.

An kuma bayyana cewa ya yi irin wannan yunkurin tun kafin faruwar lamarin a ranar Alhamis, amma abin ya ci tura. Adediji kuma ba dan gidan sarauta bane.

Sakataren fadar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bukaci mazauna garin da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa mutumin ya saci rawanin Sarki a fadar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN