Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a ya yi kira ga shugabannin Kudu-maso-Gabas da su kyale shari’ar da ake yi a kotu ta shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu a kasar.
Buhari ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin yankin Kudu maso Gabas da suka hada da shugabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a sabon gidan gwamnati da ke Abakaliki, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban wanda ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar a yau Juma'a, ya yi nuni da cewa matakin da kotu ta dauka ka lamarin Kanu shi za a bi.
Karin bayani na nan tafe...