Type Here to Get Search Results !

Da Dumi: Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya yi murabus, ya fice PDP


Rahoton da muke samu yanzun ya nuna cewa, Sanata Enyinnaya Abaribe ya fice daga babbar jam'iyyar hamayya ta kasar nan PDP, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sanata Abaribe ya kuma yi murabus daga muƙaminsa na shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ƙasar nan.

Idan zaku iya tunawa Sanatan ya janye daga shiga zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan Abia na jam'iygar PDP, wanda ya gudana ranar Laraba da ta gabata, kwana biyu da suka shuɗe.

Ya tabbatar da ficewa daga PDP da kuma murabus daga kujerar shugaban marasa rinjaye a wasu wasiku daban-daban da ya aike wa shugaban PDP na gundumarsa dake karamar hukumar Obingwa, jihar Abia.

Haka nan kuma ya aike da kwafin waɗan nan takardu ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies