Kudan Zuma sun kashe wani karamin yaro a jihar Kano, duba yadda ta faru


Wani dalibin makarantar Yanoko Nomadic Primary da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, an ruwaito cewa kudan zuma sun kashe shi. 

Sanusi Dawakintofa, kawun yaron da aka bayyana sunansa Ismail Hussaini, ya shaidawa Premium Times cewa yaron bai iya gujewa garin kudan zuman ba saboda ya samu karaya sakamakon ciwon sikila.

Hakimin garin Habibu Bello (Sarkin Fulanin Yanoko) wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an garzaya da marigayi Hussaini babban asibitin Tofa inda ya rasu da rana.

Previous Post Next Post