PDP ta yi watsi da zancen shiyya, ta jefa gasar Tikitin takarar Shugaban kasa ga kowa maimakon rabawa zuwa wani yankin NajeriyaMajalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa, ta zabi jefar da takarar neman tikitin takarar shugaban kasa a bude, maimakon a raba ta zuwa wani yanki na kasar nan.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ne ya sanar da hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, babban birn tarayya.

rayya (FCT) bayan kammala taron NEC.

Ya shaida wa manema labarai cewa matakin na daga cikin kudurorin da aka cimma a karshen taron NEC na jam’iyyar PDP karo na 96, wanda ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daban-daban.

“Bayan tattaunawa mai zurfi, NEC ta yi daidai da shawarar kwamitin shiyyar PDP na kasa na cewa a bar zaben shugaban kasa a bude. Jam’iyyar ta kuma yi aiki don ganin an cimma matsaya a duk inda zai yiwu, ”in ji sanarwar a wani bangare.

"NEC ta lura da shawarar kwamitin shiyya na cewa don tabbatar da adalci da tsari mai kyau, jam'iyyar ta dauki matakin yanke hukunci kan lokaci don hana rikitarwa ga tsarin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN