Dan jari bola ya caccaka wa matashi wuka har lahira, duba yadda ta faru

 


Wata kotun majistare da ke Makurdi a ranar Talata ta bayar da umarnin a tsare wani mai kwasar shara, Aliyu Abdullahi a gidan gyaran hali bisa zarginsa da daba wa wani matashi dan shekara 27, Rabiu Mohammed wuka har lahira.

Abdullahi, mai shekaru 23, wanda ke zaune a No. 6 Maiduguri St., Wadata, Makurdi, ana tuhumarsa da laifin kisan kai.

Babban Alkalin Kotun, Vincent Kor, bai amsa rokon wanda ake zargin na neman kada a hukunta shi ba.

Kor ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 13 ga watan Yuli domin karin bayani.

Tun da farko, Dan sanda mai shigar da kara, Insp Jonah Uletu, ya shaida wa kotun cewa wani dan uwan ​​marigayin, Mustapha Bello ne ya kai karar a ofishin ‘yan sanda na ‘D’, Makurdi a ranar 24 ga watan Mayu.

Bello ya shaidawa ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ba tare da tsokana ba, ya daba wa marigayin wuka a fuska, kunnen dama da kuma bayansa.

Ya bayyana cewa marigayin ya samu raunuka daban-daban a sakamakon harin da aka yi masa kuma ya mutu a lokacin da ake jinya a asibiti.

Mai gabatar da kara ya ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, yayin da aka kwato wukar da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Uletu ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 222 na dokokin Penal Code na jihar Benue, 2004.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN