Type Here to Get Search Results !

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun shiga jihar Kano sun kashe mutane sun sace wani Basarake


Wasu yan bindiga da ake tsammanin masu garkuwa ne sun halaka mutum Shida a wani ƙauyen ƙaramar hukumar Takai, a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Takai na yankin kudancin Kano kuma ta na da nisan kilo mita 80daga cikin kwaryar birnin Kano kuma ta haɗa iyaka da wasu garuruwa a jihar Jigawa.

Yan bindigan sun farmaki ƙauyen Ƙarfi da ke yankin karamar hukumar Takai kuma suka yi awon gaba da magajin garin ɗan kimanin shekara 53, Abdulyahyah Ilo.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga kauyen ne a kan Mashina kuma sun biyo ta Dajin Ringim daga jihar Bauchi.

Maharan sun kama hanyar futa daga ƙauyen bayan ɗaukar Basaraken lokacin da mutane suka tara Yan Bijilanti da matasa da nufin bin bayan su.

Ganin haka ya sa yan bindigan suka juyo kuma suka buɗe wa tawagar mutanen da suka biyo bayan su wuta, nan take suka harbe mutum Tara.

Daga cikin mutanen da suka harba, an tabbatar da mutum shida sun rasa rayukan su yayin da ragowar uku ke kwance a Asibiti ana kula da lafiyar su.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin kakakin rundunar yan sanda reshen Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun tura tawagar jami'an yan sanda zuwa kauyen.

Ya kara da cewa jami'an sun tafi yankin na Takai ne da nufin kuɓutar da Basaraken da aka sace kuma kame maharan baki ɗaya.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies