Da Dumi-Dumi: Wasu miyagu sun banka wa Kamfanin raba wutar Lantarkin Enugu wuta


Wasu mahara da ba'a gane ko su waye ba sun cinna wuta a Ofishin rarraba wutar lantarki na jihar Enugu da ke Ogidi, a Anambra da safiyar ranar Litinin.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa kusan kayayyaki masu amfani da Motoci 32 ne suka kone yayin harin.

Maharan sun farmakin ofishin wutar EEDC ne jim kaɗan bayan makamancin haka ta faru a Sakatariyar ƙaramar hukumar Idemili, inda wata Kotun Majistire ke ciki, duk suka haɗa suka kone su.

Da yake tabbatar da faruwar lamari, shugaban sashin hulÉ—a da jama'a na EEDC, Mista Emeka Ezeh, ya bayyana damuwarsa cewa duk kokarin sanar da hukumar kashe gobara ta Anambra bai haufar da sakamako mai kyau ba.

Ezeh ya ce ma'aikaan Kamfanin, waɗan ke wurin lokacin da abun ya faru, tilas suka zuba ido kayayyakin wurin na ƙonewa saboda babu wanda ya kawo musu ɗauki da taimako.

Ya ce:

"Har sai bayan da kwamishinan abubuwa masu amfani, Mista Julius Chukwuemeka, ya shiga tsakani da misalin ƙarfe 9:05 na safe ya kawo jami'an kashe gobar wurin."

Wane mataki hukumomi suka É—auka?

Ya ƙara da cewa wannan babban rashi ne a Kamfanin EEDC kuma koma baya a yunkurin da kamfanin yake na na inganta alaƙarsa da kwastomomi a Ogidi da Anambra baki ɗaya.

"Tuni muka jawo hankalin hukumomin da suka dace kuma muna tsammanin zasu gudanar da bincike domin kamo masu hannu a lamarin su girbi abinda suka shuka."

"Babu ta yadda tattalin arziƙin arziki kamar na su zai cigaba matuƙar za'a cigaba da samun irin haka. Mungode Allah ba wanda ya mutu sanadin lamarin, kuma mun yi Allah wadai tare da addu'ar kada haka t asake faruwa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN