Sokoto: Yadda Lauyoyi 34 suka bayyana a gaban kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi



Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Deborah Samuel, da ta durawa Annabi ashariya.

Wadanda ake zargin – Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi – wadanda kuma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa lauyoyi 34 ne suka bayyana domin kare daliban biyu da ake zargi da kashe dalibar da ta zagi Annabi, inji rahoton Sahara Repoerters

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon tayar da tarzomar da ta kai kisa da kone dalibar.

Bayan wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Khalil Musa, ya bukaci kotun da ta dage karar domin baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike.

Sai dai lauyoyin wadanda ake kara karkashin jagorancin Farfesa Mansur Ibrahim, wadanda ba su yi adawa da bukatar tsagin masu shigar da kara ba, sun roki kotun da ta bayar da belin mutanen biyu.

Hakzalika, sun bayar da misali da sashe na 157, 161(a,f) da 164 na shari’ar laifuka ta jihar Sakkwato, da kuma shashe na 36 (5) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Sai dai kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci wanda za a sanar da lauyoyin daga baya.

Don haka ta umurci wadanda ake tuhuma da a tsare su a gidan gyaran hali na Sokoto.

Karin bayani na nan tafe..

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN