
Da dumi-dumi: An banka wa motar tirela dauke da shanu wuta a Anambra bayan ta dauko su daga arewa (Hotuna)
May 08, 2022
Comment
An ga shanu suna yawo a titunan jihar Anambra bayan da wata tirela da ke dauke da su ta kone kurmus a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna tirelar na ci da wuta.
An ga shanun da suka tsere daga tirelar suna yawo a kan tituna.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a hanyar Ezinifite/Uga a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi.
0 Response to "Da dumi-dumi: An banka wa motar tirela dauke da shanu wuta a Anambra bayan ta dauko su daga arewa (Hotuna)"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka