Type Here to Get Search Results !

Da dumi-dumi: Yan daba sun kai wa ‘yan Jarida hari a wurin taron Gwamna, sun raunata biyu tare da farfasa gilasan motocinsu


Yan daba sun kai hari kan wasu motoci hudu da ke dauke da manema labarai a lokacin da suke fitowa daga wurin yakin neman zaben Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola a Gbongan, karamar hukumar Ayedaade a jihar a ranar Litinin.

Oyetola dai ya gama yi wa magoya bayansa jawabi a Unguwar Arapajo da ke Gbongan kafin aka kai wa ‘yan jarida hari.

Maharan sun yi amfani da kulake, laya, duwatsu, da gatari da su ka fasa gilasan motocin da ke dauke da ‘yan jaridan inda suka jikkata hudu daga cikinsu.

Oyetola dai ya fara yakin neman zabensa ne a Orileowu da ke karamar hukumar, inda ya yi jawabi ga magoya bayan jam’iyyar kafin ya koma Gbongan.

Za a gudanar da zaben Gwamna a Osun ranar 16 ga watan Yuli.

A halin da ake ciki, kwamishiniyar yada labarai, Misis Funke Egbemode, ta dauki biyu daga cikin ‘yan jaridan da Yan daban suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies