Bayan lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PDP Atiku ya caccaki APC, duba abin da ya ce


 Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin hada kan kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Atiku ya kuma dauki alkawarin tunkarar matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da jawabin amincewarsa bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP.

Atiku ya caccaki jam’iyyar APC kan yadda ta mayar da nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a lokacin da ta ke rike da madafun iko baya, inda ya yi alkawarin gyara su idan aka sake zabar su.

Ya ce:

“Zan magance matsalolin tsaronmu a kasar nan. Na kuma dauki alkawarin tunkarar matsalolin tattalin arzikinmu. Jam’iyyar PDP ta sanya Najeriya ta zama daya daga kasashe masu ci gaba da wadata a nahiyar Afirka.

“Mun aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka kawo ayyukan yi, da wadata a kasar nan. Jam’iyyar APC ta shigo ta goge duk wadannan nasarori. Shi ya sa na ce yau rana ce mai matukar tarihi. Domin hakan zai ba mu damar gyara duk wani rashin shugabanci na gwamnatin APC.”

Ya kuma nemi hadin kan sauran yan takara a zaben, yana mai cewa babban abun danyawa a gaba shine kwato mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.

Atiku ya ce:

"Bari na yi amfani da wannan damar wajen kira ga abokan takarata. Sannan na basu tabbacin cewa a shirye nake na hada kai da aiki tare da su sannan na basu damar taka rawa a wannan jam'iyyar da gwamnatinmu ta gaba.

“Saboda haka ’yan uwana, ina son in yaba da kokarinku na zurfafa tsarin dimokuradiyya a tsarin wannan jam’iyya. Zaben fidda gwani ne mai inganci. Don haka, na yaba muku akan haka kuma ina fatan yin aiki tare da ku kai da kai. Ta yadda za mu gina wannan jam’iyyar tare zuwa matakin da za mu iya kwace mulki.”

Ya kuma yi kira ga fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar da su ka guji kai al’amuran jam’iyyar kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN